Bayan harin ne dai Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine ya zargi Rasha kai tsaye da aikata kisan kiyashi a kan fursunoni yaki na Ukraine.
Cikin sakonsa na daren ranar Juma'a, Shugaba Zelenskyy ya ce lallai martani zai biyo bayan wannan hari da ta dora alhaki kan Rasha.
Fursunoni 53 ne dai aka tabbatar da mutuwarsu a harin, wadanda kuma a baya su ne suka yi aikin tsaro a yankin Mariopol kafin Rasha ta karbe iko da yankin cikin makonnin da suka gabata.
Kungiyar ba da agaji ta duniya Red Cross, na neman damar shiga yankin domin yi wa mutum 75 da ke fama da raunuka magani.