Shugaban Sri Lanka zai yi murabus

Shugaban Sri Lanka zai yi murabus
Rahotanni sun ce sai da jami'an tsaro suka yi harbi a saman iska domin tarwatsa masu bore da cikin fushi suka yi yunkurin afka wa gidan shugaban kan zarginsa da gaza yin katabus a tsadar rayuwar da kasar ke ciki.

Hukumomi a Sri Lanka sun tseratar da shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa daga fushin masu zanga-zanga a wannan Asabar. Dubban masu zanga-zangar sun bukaci shugaban Sri Lankar da ya yi murabus bisa zarginsa da almubazzurancin da ya jefa kasar mai mutane miliyan 22 cikin matsanancin talauci. 


Rahotannin da ke shigo mana yanzun na cewa shugaban na Sri Lanka ya amince ya yi murabus bayan bukatar hakan da 'yan majalisar kasar da jam'iyyarsa suka nuna. Dan siyasar ya ce zai dauki matakin domin wanzar da hadin kai a tsakanin 'yan kasar. 


News Source:   DW (dw.com)