Shugaban Sri Lanka ya yi murabus

Shugaban Sri Lanka ya yi murabus
Bayan kwashe lokaci na neman shugaban Sri Lanka da ya yi murabus, a karshe Shugaba Rajapaksa ya sanar da ajiye aikin nasa daga kasar Singapore.

Kakakin majalisar dokokin Sri Lanka ne ya tabbatar da murabus din Shugaba Gotabaya Rajapaksa a hukumance.

Murabus din ya zo bayan kwashe lokaci 'yan Sri Lankan na zanga-zangar neman shugabannin gwamnatin kasar da su yi adabo da mulki saboda karuwar wahalhalu.

Mr. Rajapaksa ya bayyana murabus dinsa a rubuce daga Singapore ta sakon Email da ya aike wa kakakin majalisar dokokin kasar.

Wannan ne dai karo na farko da wani shugaba ke murabus a Sri Lanka tun lokacin da kasar ta rungumi tsarin mulki na shugaba mai cikakken iko a 1978.

A halin da ake ciki dai firaministan Sri Lankan Ranil Wickremesinghe ne za a rantsar a matsayin shugaban kasa na riko, kafin a majalisar ta zabi sabon shugaba cikin kwanaki bakwai.

Yanzu dai miliyoyin 'yan kasar baki har kunne da samun labarin murabus din tsohon Shugaba Gotabaya Rajapaksa wanda ya yi kaurin suna wajen murkushe 'yan tawayen Tamil Tigers da suka addabi kasar a baya.


News Source:   DW (dw.com)