Shugaban rikon kwarya Siriya na ziyara a Saudiyya

Wannan ziyarar na zuwa ne kwanaki kalilan bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban rikon kwaryar Siriya, kasar da ta kwashe shekaru tana fama da yakin basasa.

Kafar yada labaran talabijin ta Saudiyya Al-Arabiyya ta ce shugaban na Siriya zai gana da Yarima mai jiran gado Mohammed Bn Salman, kuma akwai yiwuwar mika kokon bara na neman taimakon Riyadh a sake gina Siriya.

Al-Sharaa ya jagoranci kungiyoyin 'yan tawaye da suka kifar da gwamnatin kama karya ta Basahar al-Assad. A baya dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta yi tsami, wanda har ta kai ga cire Siriya daga kungiyar kasashen Larabawa, kafin a mayar da ita a shekarar 2023.

Karin Bayani :Taron kasa da kasa a Saudiya kan Siriya.


News Source:   DW (dw.com)