A ranar Jumma'a mai zuwa ake sa ran ganawa tsakanin Shugaba Vladimir Putin na Rasha da takwaransa Masoud Pezeshkian na kasar Iran, lokacin taro a kasar Turkmenistan da ke yankin tsakiyar nahiyar Asiya. Daya daga cikin na hannun daman shugaban kasar ta Rasha game da munufofin kasashen ketere ya tabbatar da haka a wannan Litinin.
Taron na shugabannin kasashen yankin tsakiyar nahiyar Asiya na zuwa albarkacin cika shekaru 300 da haihuwar wani ficeccen marubucin wakoki Magtymguly Pyragy. Ana sa ran karfafa hulda tsakanin Rasha da Iran lokacin ganawa tsakanin shugabannin biyu.
A makon jiya Firaminista Mikhail Mishustin na Rasha ya kai ziyara zuwa kasar ta Iran inda ya gana da shugaban kasar gami da mataimakinsa. Kasashen na Rasha da Iran suna da dangantaka mai karfi tsakanin su, inda ake zargin mahukuntan Iran da taimakon Rasha da makamai a yakin da ta kaddamar kan kasar Ukraine.