Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol ya nemi afuwar al'ummar kasar a Asabar din nan, to sai dai bai amince da yin murabus ba, yayin jawabin da aka yada ta gidan talabijin din kasar, bayan jefa ta cikin rudani sanadiyyar ayyana dokar mulkin soji, lamarin da ya janyo kiraye-kirayen murabus dinsa daga kan karagar mulki.
Karin bayani:Rikicin siyasa ya rincabe a Koriya ta Kudu
Masu zanga-zanga a kasar sun yi dafifi a bakin harabar majalisar dokokin kasar, wadda ta fara yunkurin tsige Mr Yeol, wanda jam'iyyarsa ta nemi ya ajiye aikinsa, kuma har wasu mukarrabansa ma sun fara ajiye aiki.
Shugaban ya ce hakika jawabinsa ya tunzura 'yan kasa da kuma dugunzuma tunaninsu, to amma yana neman su yafe masa.
Karin bayani:An kaddamar da gagarumin bincike kan shugaban Koriya ta Kudu
Daga cikin kujerun majalisar dokokin kasar ta Koriya ta Kudu 300, bangaren adawa na da kujeru 192, yayin da jam'iyyar shugaba Yeol ke da kujeru 108, lamarin da ke nuni da cewa makomarsa na fuskantar barazana game da yunkurin majalisar na tsige shi.