Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bukaci shugabannin siyasar kasar su kai zucciya nesa bayan rikicin da ya kunno kai a tsakanin su wanda ya kai ga wargaza gwamantin hadin gwiwa da Olaf Scholz ke jagoranta.
Shi dai Steinmeier ya karfafa fatan ganin shugabannin siyasar Jamus sun jure wa wannan yanayi da ya haifar da rashin tabbas a game da makomar siyasar kasar inda ya ce Jamus na bukatar tsayayyen rinjaye a majalisar dokoki ta Bundestag da kuma ingantacciyar gwamnatin hadin gwiwa. Shugaban kasar ta Jamus ya ce a shirye yake ya rusa majalisar dokoki ta Budestag idan har aka kai ga kada kuri'ar yanke wa gwamnati kauna.
Karin bayani: Barakar gwamnatin kawancen Jamus ta janyo cire ministan kudi
A halin yanzu ma dai, shugaban jam'iyyar CDU Friedrich Merz na matsa wa gwamnatin lamba domin a kada kuri'ar a mako mai zuwa, yayin da shugaban gwamnatin Olaf Scholz ya bukaci da a kada kuri'ar a majalisar don shirya zaben gaba da wa'adi ko zaben wuri.
Ba a dai cika samun rugujewar gwamnatin kawance a Jamus ba, amma gwamnatin da ke ci ta dade tana fama da rikici mai nasaba da sabanin ra'ayi a game da manufofin tattalin arziki da kuma shigi da ficen baki.