Shugaban kasar China ya kai wata ziyara Maroko

Shugaban kasar China Xi Jinping ya kai wa Maroko wata takaitacciyar ziyara a ranar Alhamis, kamar yadda kafofin watsa labaran cikin kasar suka ruwaito.

Mr. Xi Jinping ya samu tarba daga Yerima Moulay El Hassane a birnin Casablanca, abin da masu sharhi ke ganin an nuna karfin abota da kyakkyawar alakar da ke a tsakanin China da Morokon.

Haka nan ma shugaban na China ya gana da shugaban gwmanatin Morokon Aziz Ajanuch, kana daga bisanio ya ya karbi wata lamba ta girmamawa.

Ziyarar Shugaba Xi Jinping a Morkon dai ya yi ne bayan barin kasar Brazil inda ya halarci taron G20 na kasashe masu karfin arziki na duniya da aka yi a birnin Rio de Janeiro.


News Source:   DW (dw.com)