Shugaban Jamus ya yi kiran 'yan kasar da su hada kansu a jawabinsa na Kirsimeti

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steineimeier, ya yi kira a wannan Talata da a karkafa hadin kai bayan harin da aka kai kasuwar Kirsmeti ta Magdeburg ya fara haifar da cece-kuce a fagen siyasa yayin da ake tsaka da yakin neman zaben 'yan majalisar dokoki ta Bundestag na gabanin wa'adi da za gudanar a watan Fabarairu na 2025.

Karin bayani:Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus?  

A cikin jawabin da ya saba yi a jajibirin bukukuwan Kirsimeti, Frank-Walter Steinmeier ya bayyana bacin ransa a game da yadda harin na Magdeburg da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar tare da jakkatar wasu 200 ya rage wa bukuwan na bana armashi.

Sai dai Steimeier ya ce bai kamata ba kiyayya da tashin hankali su yi tasiri a kan Jamusawa ba, kana kuma ya yi kiran da babar murya ga al'ummar Jamus da su zama jajirtattu don jurewa wannan gwaji da wasu 'yan siyasa ke son yin amfani da shi wajen yakin neman zabe.


News Source:   DW (dw.com)