Shugaban Jamus na rangadi a Afirka

Shugaban Jamus na rangadi a Afirka
Rikicin Rasha da Ukraine su suka fi daukar hankali a ganawar da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz yayi da takwaransa na Senegal Macky Sall a birnin Dakar.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya isa birnin Dakar na kasar Senegal, a ziyararsa ta farko a nahiyar Afirka tun bayan soma mulki watanni shida da suka gabata. Rikicin Rasha da Ukraine ya mamaye taron manema labarai da shugaban gwamnatin da takwaransa Macky Sall suka yi a wannan Lahadin.

A yayin ganawar, Shugaba Sall yayi alkwarin tsoma baki a rikicin na gabashin Turai, bayan da ya ce, zai yi amfani da karfin kujerarsa na Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka, don ganin bangarorin biyu sun tsagaita bude wuta, yayi alkwarin kai ziyara a Mosko da kuma Kyiv nan bada jimawa ba.

Tun bayan barkewar yakin aka soma fargabar barazanar fuskantar matsalar karancin abinci musanman ga kasashen da ke a gabashin Afirka. Daya daga cikin muradun ziyarar Scholz a nahiyar baya ga batun tsaro da sauyin yanayi, zai kai ziyara nan gaba Jamhuriyyar Nijar da kuma Afirka ta Kudu a ziyarar ta kwanaki uku.
 


News Source:   DW (dw.com)