Shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango zai halarci taron AU

Shugaba Félix Tshisekedi na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango yana cikin shugabannin kasashen Afirka da za su halarci taron kungiyar Tarayyar Afirka da ake fara a karshen wannan makon a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, amma ba zai halarci zaman da za a yi ba kan rikicin da ke faruwa a gabashin kasarsa, inda ake zargin kasar Ruwanda da taimakon kungiyar 'yan tawayen M23.

Karin Bayani: Shugabannin Afirka sun bukaci tsagaita wuta a DRC

Birnin Kinshasa 2025 | Shugaba Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoShugaba Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango tare da shugabannin addinin KiristaHoto: DRC Presidential Press Unit

A wannan Jumma'a majalisar zaman lafiya da tsaro ta Tarayyar Afirka take zama kan rikicin na gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Ana sa ran wannan rikici zai mamaye zaman taron na kungiyar Tarayyar Afirka.

 


News Source:   DW (dw.com)