Shugaban gwamnatin Jamus na ziyarar kamfanin Ford a Cologne

A Talatar nan ce shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai kai ziyara cibiyar kera motocin kamfanin Ford na Amurka da ke birnin Cologne a nan Jamus, bayan da kamfanin ya yi ikirarin korar ma'aikata masu tarin yawa.

Karin bayani:Gwamnatin Jamus na son magance kalubalen tattalin arzikinta

A yayin ziyarar, Mr Scholz zai gana da ma'aikatan kamfanin wadanda ke cikin halin fargaba sakamakon tsoron rasa aikinsu, sakamakon shirin kamfanin na korar ma'aikata dubu goma sha biyu, daga nan zuwa shekarar 2027, wanda kungiyoyin kwadago ke matukar adawa da shirin.

Karin bayani:Shugaban gwamnatin Jamus zai sake tsayawa takara

Kamfanin Ford ya karkatar da akalar kera motocin ne zuwa ga masu amfani da lantarki wanda ta zuba jarin kudi sama da dalar Amurka biliyan biyu a cikin kamfanin na birnin Cologne, amma kuma bukatar motocin ta sauka matuka, har kamfanin ya yi wa masu saye tayin wata garabasa ta musamman idan suka saya.


News Source:   DW (dw.com)