Amurka za ta fara korar sojojin da suka sauya halittarsu daga mata zuwa mata ko maza zuwa mata nan da kwanaki 30, in ji shelkwatar tsaro ta kasar Pentagon, sai dai idan har sun samu wata kariya daga kotu.
A cikin watan Janairu ne shugaba Donald Trump ya sanar da shirinsa na korar duk wani soja da ya jirkita halittarsa ta asali da aka haife shi da ita, walau mace ko namiji, bayan ayyana dokar amincewa da jinsi biyu kadai a kasar, wace mace ko namiji ,amma banda wadanda suka sauya hallita kamar yadda aka sani a turance wato Trensgender.
Karin bayani:Trump ya haramta wa mata-maza shiga wasannin mata
Ko a cikin shekarar 2016 lokacin mulkin shugaba Barack Obama sai da rundunar sojin Amurka ta dauki irin wannan mataki na soke aikin soji ga masu sauya halitta.