Shugaban Amurka Donald Trump ya kori shugaban gamayyar ma'aikatan fadarsa Janar Charles Quinton Brown, wanda bakar fata ne, a garanbawul da ya fara yi wa dakarun sojin kasar, kasa da wata biyu da sake darewa kan karagar mulki.
Karin bayani:Donald Trump ya tsaurara kalamai a kan Zelensky
Mr Trump ne da kansa ya wallafa sakon korar babban hafsan sojin a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, tare da maye gurbinsa da Laftanar Janar Dan "Razin" Caine mai ritaya, wanda shi kuma farar fata ne, kuma a karon farko da ake nada soja mai ritaya wannan mukami a Amurka.
Karin bayani:Firaministan Burtaniya zai ziyarci shugaba Trump na Amurka
Haka zalika shugaba Trump zai maye gurbin shugabar sojin ruwan kasar Admiral Lisa Franchetti, mace ta farko da ta taba rike wannan matsayi, da kuma babban hafsan sojin saman kasar, kamar yadda shelkawatar tsaron Amurka Pentagon ta sanar, inda ta yi karin hasken cewa daga cikin wadanda za su fuskanci korar har da manyan alkalan sojin sama da na kasa.