Shugaba Xi Jinping na China zai kai ziyara kasar Rasha

Wannan taro da za a yi cikin watan gobe, ana masa kallon shiri ne a tsakanin China da Rasha da nufin rage tasirin manyan kasashe ta fuskar iko da arzikin.

Wannan ne dai zai kasance ziyara ta biyu da Shugaba Xi jinping zai kai Mosko, tun bayan kaddamar da yaki da Rasha ta yi a kan Ukraine a cikin watan Farbrairun 2022.

China dai na ikirarin zama 'yar ba ruwana a rikicin Rashar da makwabciyarta Ukraine.

A shekara ta 2006 ne Brazil ta kafa kungiyar ta BRICS, ta hada da ita kanta Brazil da Rasha da Indiya da China da ma Afirka ta Kudu wadda ta shiga a 2010.

A baya-bayan nan ta kuma samu karin mambobi da suka hada da Iran da Masar da Ethiopia da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Akwai ma kasashe irin su Saudiyya da Azerbaijan da Malasiya da ke shirin shiga cikin ta.


News Source:   DW (dw.com)