Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta Kudu, ya sanar da kafa dokar ta-baci a yankin kasar da ke fama da ibtila'in ambaliyar ruwa.
Afirka ta Kudun dai a yanzu na fama da matsala ta jin kai da Shugaba Ramaphosa ke cewa ke neman dauki cikin gaggawa.
Gabashin gabar lardin KwaZulu-Natal da birnin Durban musamman, su ne ke fama da bala'in na ambaliya na tsawon kwanaki.
Matakin kafa dokar ta bacin dai shi ne domin bai wa gwamnati damar ba da karfi ta fannin zuba kudade domin rage radadin da ambaliyar ta haddasa.
Sama da mutum 400 ne dai aka tabbatar da mutuwarsu a ambaliyar, yayin kuma da wasu kimanin 50 suka bata.