Shugaban da ke zarcewa a karo na biyu kan karagar mulki ya lashe zaben kasar da aka guudanar a ranar 24 ga watan jiya bayan da ya doke abokiyar hamayarsa Marine Le Pen ta jam'iyyar masu kyamar baki da gagrumin rinjaye.
Shugaban kotun tsarin mulkin kasar Laurent Fabius ne ya tabbatar wa Macron sabon wa'adin mulkin, bayan da ya ce ya samu rinjaye a gaban takaitattun mutanen da aka gayyata.
Duba da tanadin ayar doka ta bakwai da ta 58 da ke cikin kundin tsarin mulki, shugaban kotun tsarin mulkin ya ce "Kotu ta tabbatar da kai a matsayin shugaban kasa wanada wa'adinsa na tsawon shekaru biyar zai soma daga ranar Asabar 14 ga wannan wata.
Shugaba Macron din dai a wani takaitaccen jawabi ya bukaci hadin kan 'yan kasar tare da aiki tukuru domin kasacewar Faransa kasa mai cikakken 'yanci.