Kakakin ma'aikatar cikin gidan Tunisiya Fadhila Khelifi ta ce hukumomi sun bankado wani shiri da ya kunshi bangarori na ciki da wajen kasar da ke barazana ga lafiyar shugaban kasar da kuma tsaron kasa da nufin haifar da hargitsi. Sai dai shugaban gamayyar jam'iyyun adawa Ahmed Nejib Chebbi ya nuna shakku kan wannan sanarwa, inda ya ce wata dabara ce don gudanar da sabbin kame-kame da kuma daukar fansa kan abokan adawa.
Shugaba Saied na Tunisiya na shan suka daga bangaren 'yan adawa saboda mayar da su saniyar ware da ya yi a tattaunawar kasa kan sabon kundin tsarin mulkin da ake shirin kada kuri'ar raba gardama a kai a ranar 25 ga watan Yuli. 'Yan adawa da kungiyoyin kare hakkin bil'Adama na zarginsa da nuna son kai wajen samar da kundin tsarion mulki da ya yi daidai da muradansa.