Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa, ya lashe zaben kasar da aka kammala a yau Lahadi.
Mr. Macron ya samu kashi 58.2% cikin dari ne cikin dari na kuri'un.
Abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen wadda ta amsa shan kaye, ta samu kashi 41.8% cikin dari.
'Yar takarar adawar, Marine Le Pen, ta lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya musamman ma wajen ganin ta taka rawa a zaben majalisar dokokin kasar da ke tafe.
Tuni ma shugabannin gwamnati da hukumomi da ma 'yan siyasar nahiyar Turai suka taya Shugaba Macron murnar sake lashe zaben na Faransa.