Shugaba Biden na ziyara a Gabas ta Tsakiya

Shugaba Biden na ziyara a Gabas ta Tsakiya
Shugaban Amurka Joe Biden a wannan Laraba zai fara ziyarar rangadi a Gabas ta Tsakiya karon farko tun bayan da ya hau karagar mulki watanni 18 da suka gabata.

Zai fara yada zango a birnin Kudus na kasar Israila inda zai tattauna da Firaministan Israila Yair Lapid da shugaban kasar Isaac Herzog da kuma shugaban adawa Benjamin Netanyahu.

A ganawar da zai yi da zai yi a Israila Biden zai karfafa kudirin Amirka na tsaron Israila da cigabanta.

Haka kuma Biden zai tattauna da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a gabar yamma a ranar Juma'a inda ake sa ran zai karfafa goyon bayansa ga shirin nan na masalahar kasashe biyu da za su zauna daura da juna cikin lumana da kwanciyar hankali tare da gabatar wa al'ummar Falasdinawa damar samun tsaro daidai wa daida da yanci da kuma damammaki.

Shugaban na Amirka zai kuma kai ziyara kasar Saudiyya inda zai gana da shugabannin daular ta Saudiyya a birnin Jiddah sannan ya halarci taron koli na majalisar kawancen hadin kai na kasashen yankin Gulf.  
 


News Source:   DW (dw.com)