Shirin fitar da hatsi daga Ukraine

Shirin fitar da hatsi daga Ukraine
Wannan shi ne karon farko da za a soma fitar da kayayyakin abinci nau'in hatsi daga Ukraine tun bayan barkewar yaki a tsakanin kasar da makwabciyarta Rasha.

Ukraine ta bayar da tabbacin soma fitar da hatsi zuwa kasashen ketare daga wannan makon ne, bayan wani zama da aka yi a birnin Santanbul na kasar Turkiyya, inda Ukraine da Rasha suka cimma yarjejeniyar fitar da cimakar da ke jibge a gabar ruwan Odessa da ke Ukraine, duk kuwa da hare-haren da Rasha ke ci gaba da kai wa makwabciyarta.

Manoman Ukraine sun girbi amfanin gonar da aka kiyasta ya haura tan miliyan ashirin amma an gagara fitar da shi zuwa kasuwannin duniya saboda mamayar da Rasha ta yi wa kasar, lamarin da ya janyon tashin farashin abinci da kuma barazanar yunwa a duniya. Ana sa ran fitar da cimakar ka iya sa a samu faduwar farashin kayayyakin abinci a duniya.

 


News Source:   DW (dw.com)