Shirin fara jigilar hatsin Ukraine

Shirin fara jigilar hatsin Ukraine
Rasha da Ukraine za su rattaba hannu kan yarjejeniyar bai wa kasashen biyu damar fara fitar da hatsinsu zuwa kasuwannin duniya.

Manazarta kan lamuran siyasa na ganin yin hakan zai taimaka wajen kawo karshen takaddamar da ta janyo barazanar karancin abinci a duniya, a yayin da kasashen biyu ke ci gaba da gwabza yaki a Ukraine.

A makon da ya gabata ne dai wakilan kasashen biyu suka amince da bai wa Kiev kafar fitar da ton miliyan 22 na hatsin da ake bukata cikin gaggawa, da wasu kayayyakin amfanin gona da ke jibge a tekun Bahar Maliya saboda yakin da kasar ta tsinci kanta a ciki da makwabciyarta Rasha.

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya na daga cikin wadanda za su shaida rattaba hannun da zai gudana a birnin Istambul a wannan rana ta Jumma'a.

 


News Source:   DW (dw.com)