Shinzo Abe na cikin mawuyacin hali

Shinzo Abe na cikin mawuyacin hali
Firaministan Japan Fumio Kishida ya bayyan cewa tsohon firaministan kasar Shinzo Abe na cikin mawuyacin hali sakamakon mummnan raunin da samu biyo bayan harbinsa da wani dan bidiga ya yi.

Kasashen duniya na cigaba da nuna damuwa game da harin da aka kai wa tsohon firaministan Japan Shinzo Abe a yayin da yake tsaka da gangamin siyasa.

Babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken a yayin da yake ganawa da 'yan jarida a taron ministocin harkokin wajen G20 na birnin Bali ya ce Amirka ta kadu da jin halin da Firaminista Abe ya ke ciki, 

Da sanyin safiyar wannan Jumm'ar ce aka garzaya da tsohon firaminitan Japan Shinzo zuwa wani asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, sakamakon buda wutar da wani dan bindiga ya yi masa lokacin da yake jagorantar wanin gangamin siyasa.

 Binciken farko dai ya yi nuni da cewa maharin wani tsohon jami'in tsaro ne da ya bar aiki a shekarar 2005 


News Source:   DW (dw.com)