A wannan alhamis din aka fara bukukuwan kwanaki hudu na murnar cikar Sarauniyar Ingila Elizabeth shekaru 70 kan gadon sarauta.
Sarauniyar ta cimma nasararori da dama a tarihin mulkinta.
Sarauniya Elizabeth mai shekaru 96 a duniya, ta cika shekaru 70 da watanni kusan hudu tana sarautar da aka ce babu wanda ya yi irinta a tarihin Birtaniya.
Ta kuma fi kowane basarake dadewa a kan gadon sarauta yanzu a duniya, sannan ta ziyarci kasashe fiye da 100 a fadin duniyar.
Mai biye mata a dadewa a sarautar Ingila ita ce Sarauniya Victoria, wacce ta yi mulkin shekaru 63 da watanni bakwai da kwanaki biyu, kafin ta rasu a shekarar 1901.