Marigayi bin Zayed Al Nahyan na daga cikin shugabanin da suka farfado da kasar Emirats ta fannin tattalin arziki, da kuma dorata kan turbar kasancewa kasa mai martaba a idon duniya, inda take samun tururuwa daga 'yan kasashen ketare.
Mai shekaru 74 a duniya Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rike manyan mukamai a kasar kan ya dare kan madafan iko a shekarar 2004, bayan da ya gaji mahaifinsa Sheikh Zayed bin Sultan Al Nahyan da ya assasa kasar Dubai.
Marigayin ya rage fita a bainar jama'a tun a cikin watan Janairun 2014, bayan da ya kamu da rashin lafiya ta ciwon mutuwar rabin jiki. An ware zaman makomi na tsawon kwanaki 40 a daukacin fadin kasar don juyayin mutuwar, wacce yanzu haka ta girgiza kasashe da dama na yankin.