Kasar Senegal ta kama wani jirgin ruwa dankare da 'yan ci-rani 80 wadanda suka taso daga kasashen yammacin nahiyar Afirka a ranar Talata.
Kamen na zuwa ne sa'o'i kalilan kafun fara ziyarar Firaminstan Spain a yankin da ke funskantar karuwar 'yan ci-ranin da ke neman shiga Turai.
Senegal ta kama kwale-kwalen yan ci-rani mai shirin ketarawa
Sojojin ruwan kasar ta Senegal da ke sintiri ne suka yi kamen a kan teku mai nisan kilomita 80 daga babban birnin kasar Dakar a ranar Litinin da maraice.
Akwai mata shida da kananan yara bakwai daga cikin mutum 76 da sojin ruwan suka damke.
Sabon shugaban Senegal ya ziyarci Abuja
Fasinjojin sun hada da 'yan Senegal 55 da 'yan Guinea 11 da na Gambia bakwai da kuma 'yan Mali biyu sai kuma dan Guinea Bissau daya kamar yadda cibiyar hulda da jama'a ta sojojin kasar ta bayyana a kafar sada zumun ta X.