Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya soki abokin karawarsa Friedrich Merz na jam'iyyar CDU kan neman yin hadaka da AfD.
Scholz ya ce alkawarin da mista Merz ya dauka na cewa ba zai hada kai da jam'iyyar AfD mai kyamar baki ba abin yarda bane.
Wadannan kalaman nasa na zuwa ne makwanni biyu kafun Jamus ta gudanar da babban zabe na kasa da za a yi a ranar 23 ga watan Fabrairun 2025.
Jamus: Farin jinin CDU da CSU ya ragu gabanin zabe
A wani gangamin yakin neman zabe a birnin Potsdam na gabashin kasar, Shugaban Gwamnatin na Jamus ya fada wa kamfanin dillancin labarai na dpa cewa Merz ya karya alkawarinsa.
Jamus: Scholz ya soki Trump kan kotun ICC
A baya ana ganin Merz a matsayin wanda ka iya maye gurbin Scholz, to amma matakin da ya dauka na neman hada kai da jam'iyyar AfD ya rage mishi tagomashi tare da haddasa zanga-zanga a sassan kasar.