Scholz ya ba da sanarwar sabon taimako ga Ukraine

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya yi alkawarin samar da sabon tallafin da ya kai miliyan 650 na Yuro  ga kasar Ukraine don ta samu karfin tinkarar Rasha da ta mamaye ta tun shekaru biyun da suka gabata. A lokacin wata ziyarar ba zata da ya kai a birnin Kiyv, Scholz ya ce kasarsa Jamus za ta ci gaba da kasancewa muhimmiyar kafa ta taimaka wa Ukraine a fannin tsaro a nahiyar Turai. Dama dai wannan balaguro na kwana guda na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Ukraine ke fuskantar koma baya a fagen yaki, kuma a lokacin da ake fargabar katsewar tallafin daga Amurka idan Donald Trump ya yi rantsuwar kama aiki.

Karin bayani:  Yakin Ukraine na kara yin muni

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi amfani da wannan dama wajen nuna cewa kasarsa na bukatar karin makamai masu cin dogon zango, da kuma tabbacin samun tsaro daga kungiyar tsaro ta NATO kafin yiwuwar zama kan teburin tattaunawa da kasar Rasha. Sai dai shugaban gwamnatin Jamus ya jaddada cewar kasar ba za ta ba wa Ukraine makamai masu linzami masu cin dogon zango ba, yana mai bayanin cewa yana son kauce wa takun saka da Moscow.

Karin bayani:  Ya Koriya ta Arewa za ta sauya yakin Ukraine?

Dama dai a yanayi na tinkarar zaben 'yan majalisar dokokin da za a yi a ranar 23 ga watan Fabrairu a Jamus, Scholz na tallata kansa a matsayin shugaban da ke neman tabbatar da zaman lafiya kuma mai taka-tsantsan don kauce wa barkewar rikici tsakanin kasashen Yamma da Rasha.

 


News Source:   DW (dw.com)