Scholz na Jamus ya jaddada aniyar aiki da Trump na Amurka

A yayin da ake rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amurka a wa'adi na biyu, Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya jaddada muhimmancin dangantaka tsakanin Turai da Amurka.

Scholz ya kuma nuna irin jajircewar Amurka wajen tabbatar da dimokuradiyya da ci gaba a lokacin Jamus ta Yamma da kuma taimaka wa kungiyar tsaro ta NATO.

Donald Trump na shirin zama shugaban Amirka na 47

A cewar shugaban gwamnatin, wannan kokarin na Amurka ne ya sa tsaro ya tabbata a Jamus, bayan sake jaddada cewa Jamus din kawa ce ta kut da kut ga Amurka.

Scholz ya ce ya tattauna da mista Trump ta waya kuma sun yi magana kan muhimman abubuwa da za su taimaki kasashen nasu da kuma nahiyar Turai.

Kotu ta samu Trump da laifi amma babu hukunci

Trump wanda zai mulki Amurka a wa'adi na biyu ya ce zai fara aiwatar da manufofinsa da zarar ya kama aiki a ranar Litinin.


News Source:   DW (dw.com)