Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Firayiministan Indiya Narendra Modi suna gudanar da shawarwarin hadin gwiwa a Berlin wanda wakilai da dama na majalisar ministocin kasashensu biyu ke halarta. Wannan ne dai shawarwarin gwamnati na shida tsakanin kasashen biyu, wanda na karshe ya gudana a Indiya a watan Nuwamba 2019 shekaru uku ke nan da suka gabata.
A baya Firimiya Modi ya jaddada cewa kasarsa tana irin wannan shawarwari ne da Jamus kadai. Wannan taron zai mayar da hankali ne a kan batun hadin gwiwa a fannin tattalin arziki. A daya hannun kuma, akwai yiyuwar yakin Ukraine ya taka muhimmiyar rawa, ganin cewa har yanzu Indiya ba ta kakaba wa Rasha takunkumi bayan da ta mamaye Ukraine ba.