Hukumar Tarayyar Turai ta gabatar da sauyi kan shirin saka takunkumi kan bangaren makamashin kasar Rasha, inda Hungary, Slovakia da Jamhuriyar Czech za su samu karin dama ta ci gaba da saya zuwa lokacin da za su sauya inda suke samun makamashi.
Manyan jami'an Tarayyar Turai suna fata wannan zai zama mataki mafi tsauri da kungiyar ta dauka kan Rasha tun bayan da kasar ta kaddamar da kutse a kan kasar Ukraine.
Ana sa ran kara tattaunawa kan daftarin a wannan Jumma'a tsakanin kasashen mambobin kungiyar ta Tarayyar Turai, mai yuwuwa ta kai zuwa karshen mako.
Daukacin kasashe mambobin kungiyar 27 ana sa rana za su nuna sassauci domin samun matsaya zuwa mako mai zuwa.