Sauye-sauyen ministocin Siri Lanka

Shugaba Anura Kumara Dissanayake na kasar Siri Lanka ya bai wa kansa mukamun ministocin ma'aikatun kudi da tsaro a sauye-sauyen majalisar ministoci da ya yi a wannan Litinin. Haka ya biyo bayan nasarar da jam'iyyar shugaban ta samu a zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar, wanda shugaban ya kira gabanin karewar wa'adin majalisar dokokin kasar.

Karin Bayani: Tsugune ta gaza karewa a Siri Lanka

Shugaban mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai ya kuma sake nada Harini Amarasuriya matsayin firiministar kasar. Shugaba Anura Kumara Dissanayake na kasar Siri Lanka ya kira zaben watanni 10 gabanin karewar wa'adin majalisar dokokin kasar, domin shugaban ya samu rinjayen da yake bukata wajen aiwatar da sauye-sauyen bunkasa tattalin arzikin kasar da ke cikin mawuyacin hali.

 


News Source:   DW (dw.com)