Sanarwar da rundunar sojin kasar ta bayyana ta ce an samu sauye-sauye na musamman ga shugabannin bataliyoyin da ke Legas, hedkwatar tattalin arziki kasar da Enugu a kudu maso gabashin kasar, da kuma Kaduna da ke a arewa maso yammacin kasar. Wannan sanarwa na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin kasar ke fuskantar sukka daga dukkanin bangarori saboda abin da suka kira gazawa na dakile matsalar rashin tsaro. A makwannin da suka gabata kungiyar IS ta kai wani kazamin hari a wani gidan yari da ke wajen birnin Abuja a Kuje, da ke da nisan kilomita 40 daga fadar shugaban kasar, abin da ya janyo wata sabuwar muhawara a kan sha'anin tsaro a Najeriyar