Saura kiris a cimma tsagaita wuta a Gaza - Blinken

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce "saura kiris" a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza na Falasdinawa.

Ko da yake mista Blinken ya sake nanata cewa ba lallai ne hakan ya samu ba kafun shugaba Biden na Amurkar ya mika ragamar kasar ga Donald Trump mai jiran gado.

Blinken ya kammala rangadi na 11 kan rikicin Gaza ba tare cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba

Ya shaida wa masu aiko da rahotanni cewa a Gabas ta Tsakiya "za a cimma tsagaita wuta sannan a sako fursunonin yaki da ake rike da su."

Kalaman na Blinken na zuwa ne a lokacin da sojojin Isra'ila suka sanar da gano wata gawa daga cikin mutanen da ke hannun Hamas a zirin Gaza.

Hamas ta saki bidiyon 'yar Isra'ila da ake garkuwa da ita

Mai magana da yawun rundunar sojin ya ce gawar ta wani Balarabe ne dan Isra'ila mai suna Yosef AlZayadni dan shekara 53 kuma har yanzu babu tabbacin halin da dansa da aka kamasu tare ke ciki.


News Source:   DW (dw.com)