Saudiyya ba ta samun kujera a Hukumar Kare Hakkin Bil'adama

Dama dai, kungiyoyin kasa da kasa da suka himmatu wajen kare hakkin bil'adama sun yi tir da hukunce-hukuncen kisa guda 214 da Saudiyya ta aiwatar a cikin wannan shekara ta 2024. Tuni dai kungiyoyin masu zaman kansu irin su Reprieve da ESOHR sun bayyana gamsuwa bayan da suka danganta Yarima mai jiran gado Mohammed ben Salman da aikata munanan laifukan take hakkin dan Adam a Saudiyya.

Karin bayani: Hukuncin kisa na matukar karuwa a duniya

Sai dai duk da shafa wa wasunsu kashi kaji kan kare hakkin bil'adama, amma daukacin kasashen Afirka biyar da suka yi takara sun samu kujerar a hukumar, ciki har da Benin da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Habasha da Gambiya da Kenya. 

A yankin Latin Amurka da Caribbean kuwa, an zabi Boliviya da Kwalambiya da Mexico yayin da a gabashi da Yammacin Turai kuwa, Jamhuriyar Czek da Arewacin Macedoniya da Iceland da Spain da Switzerland ne suka samu kujerau a Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya.

Wannan hukuma mai mambobi 47 da ke da mazauni a birnin Genava na yawan fuskantar kace-nace tsakanin gwamnatocin da ke bin tafarkin dimukuradiyya da 'yan kama-karya.

 


News Source:   DW (dw.com)