Saudi Arebiya da makwabtanta na Gulf sun ga watan Ramadan

Saudi Arebiya da makwabtan kasashen Gulf sun sanar da ganin jaririn watan Ramadan a wannan Juma'a, wanda ke nuna cewa Asabar za a tashi da ibadar Azumi, wato daya ga watan Ramadan.

Sauran kasashen da suka bi sahunta sun hada da Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Oman, Jordan da Syria, inda kasashen musulmi da dama na duniya suka shiga cikin jerin wadanda suka sanar da fara daukar Azumin ranar Asabar din.

Yayin da shi kuma jagoran mabiya Shi'a na kasar Iraqi Ayatollah Ali al-Sistani ya sanar da cewa za su fara na su Azumin a ranar Lahadi mai zuwa.


News Source:   DW (dw.com)