Sheikh Mohamed wanda aka fi sani da ‘MBZ' ya gana da ‘yan majalisar koli ta tarayyar kasar da suka kunshi sarakunan masarautun Hadaddiyar Daular Larabawa guda bakwai, a dai-dai lokacin da kasar ta shiga cikin zaman makokin rasuwar dan uwansa Sheikh Khalifa wanda ya rasu ranar 13 ga watan Mayu shekarar 2022.
Majalisar kolin kasar ta zartas da wannan hukunci ne bayan shafe shekaru yana ta kiraye-kirayen ba shi mukamin daga bayan fage yayin da dan uwansa Sheikh Khalifa ya koma gefe saboda rashin lafiya.
Sabon Shugaban kasar Sheikh Mohamed yana daya daga cikin manyan shugabannin kasashen Larabawa, ya kammala karatun digiri na kwalejin soja ta Birtaniya wato Sandhurst, yana jagorantar daya daga cikin rundunar sojojin da suka fi kayan aiki a yankin Gulf.
Abu Dhabi, wanda ke rike da mafi yawan arzikin man fetur na kasashen yankin Gulf, ya rike mukamin shugaban kasa tun bayan kafa Tarayyar Hadaddiyar Daular Larabawa da mahaifin Sheikh Khalifa, Marigayi Sheikh Zayed bin Sultan Al Nahyan, ya kafa a shekarar 1971.