Daruruwan mutane ne cikin murna suka tarbi Sarki Charles na Burtaniya da sarauniya Camilla a Lahadin nan a birnin Sydney na kasar Australia, lokacin da ya kai ziyara mujami'ar St Thomas' Anglican Church, inda ya bayyana jin dadinsa a fili game da tarbar da ya samu.
Karin bayani:Sarki Charles na Ingila na ziyara a Kenya
Wannan ita ce ziyarar sarkin ta farko a kasar waje, tun bayan da ya kamu da cutar kansa, kuma wannan ce ziyararsa ta 16 a kasar Australia, wadda ya yi karatu a cikinta lokacin yana matashi a shekarar 1966.
Karin bayani:An nada Sarkin Ingila bayan shekaru 70
Haka zalika sarki Charles ya kai ziyara majalisar dokokin jihar New South Wales, wadda ke bikin cika shekaru dari biyu da kafuwa.
Bayan kammala ziyarar ta kwanaki 6 ne sarkin zai halarci taron kungiyar kasashen rainon Ingila ta Commonwealth, da za a gudanar a Samoa.