Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ba za ta halarci zaman bude majalisa ba

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ba za ta halarci zaman bude majalisa ba
A karon farko sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ba za ta hallarci bikin bude majalisa ba bisa wasu dalilai da ke da nasaba da lafiya a cewar sanarwa da fadar Buckingham ta fidda.

Sarauniyar da aka jima ba a ganta a bainar jama'a ba tun bayan wata jinya da ta yi a watan Oktoban shekarar da ta gabata. Rahotanni na nuni da cewar tana fama da karancin lafiya sai dai ba a fayyace me ke damunta ba.

Yarima Charles ne zai wakilci mahaifiyarsa, Sarauniya Elizabeth da ke da shekaru 96, wanda kuma zai karanta jawabin sarauniyar a gaban majalisar dokokin kasar a gaba a yau Talata.

A watan gobe na Yuli ne za a gudanar da gagarumin bikin cika shakaru 70 da Sarauniyar ta kwashe tana kan kujerar sarauta masarautar Birtaniya.
 


News Source:   DW (dw.com)