Saurauniyar wacce ta janye daga harkokin gudanar da masarautar saboda matsalar kafafu da tsufa wadda ke yin amfani da keken guragu wajen yin kai da kawonta, a wannan rana ta Alhamis ta cika shekaru 96. Tun a cikin watan Oktoba, ta wakilta danta yarima Charles, mai shekaru 73, wanda zai gajeta domin tafiyar da harkokin mulki.
An dai shirya yi mata biki na musammun, inda za a yi harbin igwa daga hasumiyar fadar Hyde Park da ke a birnin London domin nuna murnar zagayowar ranar haifuwarta.