Samamai 160 lokaci guda kan 'yan Mafiya

Izuwa yanzu kamfanoni kimanin 400 ne da kuma mutane 200 ake bincikensu kan aikata laifuka mabanbanta musamman ta kan yanar gizo. Manufar samaman dai ita ce gano mabuyar 'yan mafiya, inda suke bincikar kungiyoyin da ake zargi suna da wata dabarar yin zamba a fadin Turai. Sai dai baya ga kasashen Tarayyar Turai jam'an tsaro na zargin kungiyar tana da rassa a Hadaddiyar Daular Larabawa, inda suke amfani da na'urorin zamani wajen cutar jama'a ta hanyoyi daban-daban. Daga cikin ayyukan da suke yi harda taimakawa kamfanoni su iya kaucewa biyan haraji ko kudin fito, wanda kuma hukumomi basa iya ganewa komin girman kasuwanci da kamfani ya yi. Bincikin da aka kaddamar ya shafi wurare 160 kama daga kasar Italiya inda 'yan Mafiya suka fi karfi, izuwa kasashen Spain, Luxembourg, Jamhuriyar Czech, sai kuma a kasashen Slovakiya, Croatiya, Bulgariya, Cyprus, Netherlands,  Switzerland da kuma a Hadaddiyar Daular Larabawa


News Source:   DW (dw.com)