Haka nan ma wasu manyan mutane uku na daga cikin wadanda suka halaka, baya ga dinbin wadanda suka samu munanan raunuka. Tuni dai aka bayyana maharin da wani matashi dan asalin jihar, mai shekaru 18 da haihuwa. Jim kadan bayan dawowarsa daga ziyarar aiki da ya kai kasashen Asiya, Shugaba Joe Biden na Amirkan ya yi jawabi ga al'ummar kasar tare da bayyana cewa akwai bukatar gaggauta samar da tsauraran dokoki kan mallakar bindiga.
Rahotanni daga jihar Texas da ke Amirka, na nini da cewa yara 18 na daga cikin sama da mutane 20 da suka halaka yayin wani harbin kan mai uwa da wabi a wata makarantar firamare.