Rahotanni sun ce bayan da kura ta lafa fursunoni 49 ne kawai aka iya samu daga cikin 872 da ke cikin gidan yarin na yankin Beni da ke gabashin Kwango.
Mai magana da yawun sojoji a yanknin Beni, Antony Mualushayi, ya sanar cewa lamarin ya faru ne a gidan kason Kakwangura da ke yankin Mutembo. Jami'in ya zargi wata kungiyar sakai ta Mai-Mai da kai harin a wannan yanki na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ke fama da fitintunu. Sai dai wasu masana na zargin kungiyar 'yan tawayen ADF da kitsa kubutar da fursunonin.