Sakamakon zabe ya fara fitowa a Kenya

Sakamakon zabe ya fara fitowa a Kenya
Manyan 'yan takara biyu na tafiya kafada-da-kafada da juna, inda jaridar Daily Nation ta Kenya ta ce mataimakin shugaban kasa William Ruto na da 48% yayin da tsohon firaminista kuma madugun adawa Raila Odinga ke da 48 %.

Sakamakon zaben da ya fara fitowa a Kenya kawo yanzu na nuna cewa mataimakin shugaban kasa William Ruto na gaban  tsohon firaminista kuma madugun adawa da ke samun goyon bayan shugaban kasa Raila Odinga..

Hukumar zaben kasar ba ta kammala tattara sakamakon zaben da aka gudanar a rumfuna sama da 40,000 ba. Amma dokar zaben Kenya na bukatar dan takara ya samu rinjaye da fiye da kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada kafin a ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara ko kuma aje zagaye na biyu.

Jama'ar Kenya na ci gaba da dakon kammalallen sakamakon zaben shugaban kasa, a daidai lokacin da masana ke kira ga magoya bayan 'yan takara da su kai zuciya nesa don kauce wa rikicin bayan zabe.


News Source:   DW (dw.com)