Shuganba Anura Kumara Dissanayaka mai shekaru 55 a duniya dan jam'iyyar masu ra'ayin rikau ya sha rantsuwar kama aiki bayan da hukumar zabe ta kasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a ranar Lahadin da ta gabata.
Anura Kumara Dissanayaka ya karbi madafun iko a daidai lokacin da kasar Sri Lanka ke fama da gagarumar matsalar karayar tattalin arziki mafi muni a cikin tarihinta.
Karin bayani: Sri Lanka ta mika kokon bara ga IMF
Hasali ma wannan matsala ce ta tayar da guguwar rikicin siyasa da ta yi awon gaba da tsohon shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa daga mukaminsa bayan gagarumar zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da kuma yankewar kayan masarufi a kasawannin kasar.
Karin bayani: Shugaban Sri Lanka ya yi murabus
Sake tayar da komadar tattalin arzikin Sri Lanka da daya daga cikin mayan kalubalai da ke gaban Anura Kumara Dissanayaka wanda tun tuni ya yi alkawarin rage haraji a kan kayan masarufi domin rage wa 'yan kasar radadin tsadar rayuwar da suka fada yau da shekararu biyu kenan.