Mutanen na ficewa ne sakamakon yadda aka kwashe kwanaki biyar ana gwabza fada tsakanin dakarun mataimakin shugaban kasar Riek Machar,da na magabtansa da suka bi bayan sahun shugaba Salva Kiir a garin Leer da ke a kudancin kasar inda nan ne mahaifar Riek Mashar. Wani shaidu ya shaida wa kamfanin dilamcin labaran na Faransa AFP cewar sojojojin sun kai harin a kauyukansu suka kona gidaje tare da kwashe shanu da awaki. A cikin wata sanarwa da ya bayyana wakilin MDD a Sudan ta Kudu ya ce an wawashe kauyuka da dama da ke kudu da garin Leer da kuma lalata tashar jiragen ruwa ta Adok da ke a kan gokin Nilu, sai dai bai bayyana wanda ke da alhakin yin haka ba.