Sabon rikici ya barke a gabashin Kwango

Sabon rikici ya barke a gabashin Kwango
'Yan tawayen M23 da dakarun gwamnatin Kwango sun cigaba da luguden wuta a gabashin kasar, duk da yunkurin shugabannin kasashen biyu na kawo karshen rikicin.

Kungiyar 'yan tawayen M23 da Kwango ke zargin Ruwanda da goyon bayanta, ta fara wani gagarumin farmaki a kan iyakar gabashin kasar a karshen watan Maris na 2022, inda ta kwace wani muhimmin shingen kan iyaka da wasu garuruwa duk da kokarin da sojoji suka yi na dakatar da su.

Kasar Ruwanda ta musanta goyon bayan kungiyar M23, sannan ta zargi Kwango da yaki da wata kungiyar da ke dauke da makamai da nufin kwace mulki a Kigali.

Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame da takwaransa na Congo Felix Tshisekedi, sun gana a Angola a ranar Laraba 06 ga watan Yulin 2022 inda suka amince da taswirar hanya da ta hada da dakatar da fada nan take da kuma ja da baya.


News Source:   DW (dw.com)