Ruwanda ta sallami manyan hafsoshin tsaronta

Shugaban kasr ta Ruwanda Paul Kagame, ya amince da murabus din Janar Jean Bosco Kazura da karin wasu sojoji dubu da 162 masu sauran mukamai.

Shi dai Janar Kazura, mai shekaru 62, kafin murabus din nasa, shi ne hafsan hafsoshin kasar, mukamin da ya rike tsakanin shekarar 2019-2023.

Haka nan ma ya taba zama mai bai wa shugaba Kagamen shawara kan harkokin soja, sannan ya jagoranci rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD a Mali a tsakanin 20213-2014.

Shi dai Shugaba Paul Kagame, ya zargi sojoji da dama ne da rashin da'a, abin kuma da ya sanya shi daukar matakin a cewarsa.


News Source:   DW (dw.com)