Gwamnatin Jihar Pernambuco, wadda Recife ce babban birninta, ta bayar da rahoton bacewar mutane 14, yayin da ake ci gaba da bincike a yankunan da lamarin ya fi shafa domin gano ko akwai masu sauran shan ruwa a gaba. Kwararru a kan sha'anin kare muhali sun ce dummamar yanayi da rikedewar dazuzzuka zuwa birane na daga cikin dalilan da suka janyo saukar ruwan sama da ya wuce kima.