Faduwar ginin dai ya rutsa da mutanen bakwai a ciki inda jami’an biyu daga cikinsu suka mutu yayin da jami’an hukumar kai daukin gaggawa ta Abuja suka samu ceto mutane biyar daga baraguzan ginin.
Ginin da aka tsara shi a yanayi na kasuwar zamani da ke da shaguna, ya fadi ne a yayin da ake sanya masa daben zamani watau gab da kamala aikinsa ke nan.
Ya zuwa yanzu ba akai ga sani dalilin faduwar wannan ginin ba. Ana yawan samun faduwar gini a Najeriya, musamman a yankin kudancin kasar.